Dukan halittu suna samun rai ta wurin uwayensu. Ko da ƙanƙantar halitta, uwa tana da ƙaunar uwa mai zurfi wadda ke ba ta damar sadaukar da rayuwarta ga 'ya'yanta. Me ya sa Allah ya halicci dukkan abubuwa don su sami rai ta wurin uwayensu? Kuma me ya sa uwaye, har ma da uwayen ƙananan halittu, duk suke da ƙaunar uwa? Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa da nufinsa, ya bayyana mana hanyar samun rai madawwami, ta wurin ƙa'idar haihuwa a wannan duniyar da kuma ta wurin ɗabi'a mai daraja ta Allah Uwa. Dukan halittu za su iya rayuwa ne kawai gwargwadon tsawon rayuwar da suka samu daga uwayensu. Haka nan, za mu iya samun rai madawwami ta wurin Uwarmu ta ruhaniya. Wannan kuwa saboda Allah Uwa ce kaɗai, wadda take da rai madawwami, za ta iya ba mu rai madawwami. A wannan zamani, dole ne mu zama 'ya'yan Allah Uwa don mu sami rai madawwami. Ku zo ikkilisiyar Allah wadda ta yi imani da Allah Uwa
경기도 성남시 분당구 성남분당우체국 사서함 119
Tel 031-738-5999 Fax 031-738-5998
총회: 경기도 성남시 분당구 수내로 50(수내동)
대표교회: 경기도 성남시 분당구 판교역로 35(백현동 526)
ⓒ World Mission Society Church of God. 모든 권리 보유. 개인정보처리방침